Daga Aisha Aliyu Umar
Matashin nan dan Kano mai suna Suleiman Isah da ya auri wata Ba’amurkiya, Janine Reimann ya shiga aikin sojan Amurka.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa a ranar 13 ga Disamba, 2020, Sulaiman Isah, wanda a lokacin yana da shekaru 23, ya auri Ms Reiman, mai shekaru 46.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, masoyan biyu sun hadu ne a dandalin sada zumunta na Instagram watanni 10 kafin aurensu.
Ba maniyacin da zai biya karin kuɗin aikin Hajjin bana – NAHCON
Reiman, mai sana’ar dafa abinci a Lindon, California, daga baya ta tashi zuwa Najeriya don bikin auren.
Daurin auren, wanda ya gudana a Masallacin Barikin Panshekara, ya samu halartar manyan baki da dama, ciki har da tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani.
Sai dai kuma Isah ya tabbatar da samun aikin sojan a jiya Juma’a bayan da ya wallafa hoton sa sanye da kakin sojojin Amurka a facebook hotonsa a shafinsa na Facebook.
Ya wallafa hoton tare da cewa, “Alhamdullillah- na gode”.
Don haka abokansa da masu fatan alheri sun mamaye sashin sharhi da sakonnin taya murna