Daga Safiyanu Dantala Jobawa
Ajiyan Masarautar Rano kuma hakimin karamar hukumar Garum Malam Alhaji Lawan Abubakar Madaki ya bukaci masu rike da mukaman gargajiya da su rinka jaddada al’adunsu don kara ingantasu a kodauye.
” Dabbaka al’adu na Kara fito da kima da martaba kowacce kabilanci musamman a idon baki , rashin yin hakan kuma na taimakawa wajen zubewar kimar kowacce kabilanci, sannan kuma akwai yiwuwar wata rana a wayi gari a rasa al’adun”.
Hakimin na Garum Malam ya bukaci hakan ne yayin wani bikin Daba karo na farko wanda ya gudana a juma’ar da ta gaba a yankin.
Matashin nan da ya auri baturiya yar a Kano ya zama soja a Amurka
Hakimin ya ce yin bikin daba na kara zumuncin juna tare da karo hadin kai ga al’umma, sannan nan ya kara farfado da cigaban al’adun Hausawa da tarihinsu tare da sanin shuwagabaninsu da kuma martabarsu a idanun duniya.
Alhaji Lawan Abubakar ya kuma gode wa majalisar masarautar Rano, karkashin jagorancin mai martaba sarkin Rano, Alh Kabiru Muhammad Inuwa a bisa amincewarsa wajen ganin an gudanar da bikin dabar.
“Ya gode wa yan majalisarsa abisa irin hadin kan da suke ba shi don tafiyar da mulkin jama’a cikin gaskiya da amana”.
Hakimin na Garun malam, ya kuma godewa al’umman yankin dangane da fitowa da suka yi don gudanar da wannan bikin na Daba.
Bikin Dabar na Garun malam ya sami halartar jama’a da dama daga sassa daban-daban dake kewaye da karamar hukumar.