Daga Auwal Alhassan Kademi
Rundunar ‘yan sanda ta Najeriya reshen babban birnin tarayya Abuja, ta ce ta kuɓutar da akalla mutane 58 da aka yi garkuwa da su a dajin Udulu na ƙaramar hukumar Gegu a jihar Kogi, wanda ya yi iyaka da dajin Sardauna dake jihar Nasarawa.
‘Yan bindigar da suka fuskanci an fi ƙarfinsu sai suka tsere da harbi da dama a jikinsu, tare da barin mutanen da suka yi garkuwar da su.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ta rabawa manema labarai.
Da dumi-dumi: Yan Sanda a kano sun kama matashin da ya kashe mahaifiyarsa da wuka
Ta ce masu garkuwar da ɓarayin daji sun fara harbin tawagar jami’an tsaron a lokacin samamen da ‘yan sandan suka kai, abin da ya kai ga musayar wuta daga ɓangarorin biyu.
Sanarwar ta ce an samau nasarar ceto mutanen ne sakamakon haɗin giwwar ‘yan sanda da ‘yan sintiri da da mafarauta daga ƙauyuka daban-daban na Abuja, domin daƙile irin waɗannan laifuka da kuma kama masu aikata hakan don gabatar da su a gaban shari’a.
Bankwana: Ganduje ya yafewa malaman makaranta kudaden gidaje
Kwamishinan ‘yan sanda na Abuja CP Haruna Garba ya ce za su ci gaba da aiki tuƙuru domin ceto duk wanda aka ji labarin an yi garkuwa da shi, tare da kama masu wannan aiki.
CP Haruna ya kuma buƙaci mutane da su sanya idanu tare da kai ƙorafin duk wasu mutanen da ba su yadda da sintirinsu ba, ta hanyar wasu lambobin waya da rundunar ta ware.