Gwamnatin kano ta kaddamar da kwamitin yaki da cin zarafin ‘ya’ya mata

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Ma’aikatar harkokin mata da ci gaban al’umma ta jihar Kano, ta kaddamar da kwamitin kula da dabarun sarrafa ilimin dabarun yaki, kan cin zarafin mata .

 

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’ar hulda da jama’a ta ma’aikatar harkokin mata ta jihar Kano, Bahijja Malam Kabara wadda kuma ta aikowa kadaura24 a Kano.

Bankwana: Ganduje ya yafewa malaman makaranta kudaden gidaje

Sanarwar ta bayyana cewa, kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban jama’a Dr. Zahra’u Muhammad Umar ce ta kaddamar da kwamitin a asibitin koyarwa na Aminu Kano.

Kannywood: Tarihin Rayuwar Jaruma Rahama Sadau

Kwamishiniyar wadda babbar sakatariyar ma’aikatar Dr Sa,adatu Sai’d Bala ta wakilce ta, ta bukaci mambobin kwamitin da su yi aiki tukuru domin dakile matsalar cin zarafin mat, saboda yadda dabi’ar take kara karuwa a jihar.

Kwamishiniyar, ta shawarce su da su mai da hankali kan sauran laifukan cin zarafi da suka shafi jima’i, cin zarafi da sauran kalubale a fadin jihar da kasa baki daya.

Dokta Zahra’u ta yi nuni da cewa, an zabo mambobin kwamitin bisa la’akari da kwarewar da suka samu a matsayin abokan hadin gwiwa wajen tallafawa manufofi da shirye-shirye da nufin daukaka darajar rayuwa a tsakanin ‘yan jihar Kano.

Malam Yakubu Muhammad, Daraktan tsare-tsare da bincike da kididdiga na ma’aikatar harkokin mata da ci gaban jama’a ta jihar kano ya gabatar da makala kan yadda ake bayar da rahoton bayanai.

wata kungiya mai zaman kanta ta George town Global Health, Najeriya ita ma ta gabatar da makala yayin taron.

Mambobin kwamitin sun hada da wakilai daga, NAPTIP, ‘yan sanda, ma’aikatun lafiya, ilimi, harkokin mata, kungiyoyi masu zaman kansu da duk masu ruwa da tsaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ba zaben 2027 ne a gaba na ba – Tinubu

    Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu...

Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano kuma...

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya tura tawaga mai karfi wajen Abba Ganduje

Daga Rahama Umar Kwaru   Babban Daraktan Hukumar Samar da Wutar...

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...