Babban jami’in ba da agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya , ya bayyana cewa zai yi wuya a kawo karshen faɗan da ake gwabzawa a Ƙasar Sudan, saboda ɓangarorin da ke rikici da juna ba su nuna yunkurin hakan ba.
Ya ce akwai damuwa matuka na yadda rikicin ke ci gaba da yaɗuwa.
Martin Griffiths yana magana ne da BBC bayan ya ziyarci Port Sudan da ke gaɓar tekun Bahar Maliya.
Da dumi-dumi: Allah kadai yasan jam’iyyar da zan mikawa mulkin Kano – Ganduje
“Kuma duk wata hanya ta samar da tsagaita wuta a ƙasar ya citura saboda ɓangarorin sun ki amincewa da hakan,” in ji Martin
Ya ce ya kirayi janar-janar ɗin da ke faɗa da juna da su zauna teburin sulhu wajen ganin an kai kayan agaji cikin gaggawa da kuma shawo kan rikicin.
Ya ce ɓangarorin biyu da ke gaba da juna sun yi magana game da ra’ayinsu kan ka’idojin jin kai – amma da alama ba a yi niyyar kawo karshen yakin ba.
Ana shirin soma wani sabon tsagaita wuta na kwanaki bakwai – amma tsagaita wuta da aka cimma a baya ta ruguje.