Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa bai da tabbacin gwamnatin jam’iyyar da zai mikawa mulki a ranar 29 ga watan mayun shekarar 2023.
” Ina fata gwamnatin da zata gajeni ko ta NNPP ko ta APC Allah ne kadai ya sani, Amma dai Ina fata zasu karasa aiyukan da muka bari bamu karasa ba, kamar yadda muma muka yi”. Inji Ganduje
Rashin kishin kano ne zai sa mutum ya rushe Ginin da mukai a tsohuwar Daula Otel – Ganduje
Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da yake bude titin Ahmadu Bello way a wannan rana .
Gwamnan yace kowacce gwamnati ta kan tafi ta barwa ta bayan ta aiki, don haka ba sabon abu bane, kawai abun da ya ke fata shi ne kar Abar aiyukan da ya faro don gudun barnatar da kudaden al’umma jihar kano.
” Mun gudanar da aiyuka Masu tarin yawa a wa’adin gwamnatin na, kuma dukkanin kananan da manyan aiyukan na yi Imani zasu taimaka wajen inganta kasuwanci da tattalin arzikin jihar kano da na kasa baki daya”.
Ganduje ya bude aiyukan titin da ya tashi daga Goron dutse zuwa kasuwar kurmi wato Sheikh Mahmoud Salga Road dake karamar hukumar Dala da titin Kwarin akuya dake karamar hukumar Fagge, sai kuma titin Gashash Road dake Nasarawa GRA da Kuma na Ahmadu Bello way.