Daga Halima Musa Sabaru
Jami’ar jihar Imo dake Owerri ta dakatar da daya daga cikin malamanta, mai suna Desmond Izunwanne, bisa zarginsa da mari wasu dalibai mata wadanda suka shiga aji a makare sanye da kayan makarantar sakandire.
Kakakin Jami’ar, Ralph Njokuobi, a wata sanarwa da ya fitar a Owerri, babban birnin jihar, ya ce matakin da malamin ya dauka “abin kunya ne kuma bai dace ba.”
Rashin kishin kano ne zai sa mutum ya rushe Ginin da mukai a tsohuwar Daula Otel – Ganduje
Sanarwar ta ce a taron gudanarwar jami’ar ta amince da dakatar da malamin nan take .
Kakakin jami’ar ya kuma sanar da cewa an kafa kwamitin ladabtarwa na mutune uku don “gano musabbabin faruwar lamarin ,” in ji sanarwar.
“A karshen taron hukumar gudanarwar da aka gudanar a ranar Talata 2 ga watan Mayu 2023, hukumar ta amince da dakatar da malamin, Dokta Desmond lzunwanne, tare kuma da kafa kwamitin ladabtarwa na mutum uku don bankado dalilan da ya haddasa al’amarin.