Daga Rahama Umar Kwaru
Ma’aikatar tsaron kasar Turkiyya ta bayyana cewa an harbi wani jirgin sojin Turkiyya da ke aikin kwashe ƴan kasar Turkiyya daga Sudan da ke fama da rikici.
Jirgin mai lamba C-130 na Turkiyya ya nufi sansanin jiragen sama na Wadi Seidna domin kwashe ƴan kasarsa da ke birnin Khartoum.
Sai dai kuma rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya ci karo da harbin kananan bindigogi, a cewar sanarwar da ma’aikatar tsaro ta Turkiyya ta fitar a ranar Juma’a.
Shugabancin majalisa: Abubuwan da aka tattauna tsakanin Tinubu, Akpabio da Barau Jibri
Sanarwar ta kara da cewa, a cewar TRTWorld jirgin ya sauka lafiya, kuma ba a samu wata matsala ba.
A yayin mayar da martani kan rahoton, sojojin Sudan sun zargi dakarun sa-kai na Rapid Support Forces, da harbin jirgin sojin na Turkiyya.
Sai dai kuma RSF din ta musanta cewa ta harbo jirgin inda ta nace cewa sojojin Sudan na yada karya.