Daga Aisha Aliyu Umar
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin 1 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu domin bikin ranar ma’aikata ta bana.
Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya.
Ministan, a wata sanarwa dake dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida, Shu’aib Belgore a ranar Juma’a, ya yabawa ma’aikatan kan kwazonsu da sadaukarwa.
Sarkin kano ya nada sabbin Hakimai guda shida
Sanarwar ta umurci ma’aikata da su kara himma wajen gudanar da aiyukan su kamar yadda suka Saba don inganta aikin gwamnati da Kasar nan baki daya.