Sarkin kano ya nada sabbin Hakimai guda shida

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, ya nada sababbin Hakimai guda shida.

Da yake jawabi lokacin da aka nada Hakiman, Mai Martaba Sakin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yace an nadasu Sarautun ne bisa cancantarsu da irin gudunmawar da suke bayarwa a cikin al’umma.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren yada labaran Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24.

Yakin Sudan: Rukunin farkon na daliban Najeriya sun Isa Ƙasar Masar – Gwamnatin tarayya

Wadanda aka nada Sarautun sun hadar da Alhaji Abbas Maje Ado Bayero a Matsayin Bauran Kano da Alhaji Kabiru Ado Bayero a Matsayin San Turakin Kano da Alhaji Umar Ado Bayero wanda aka nada shi Yariman Kano.

 

Sauran sune Alhaji Tijjani Ado Bayero a Matsayin Zannan Kano da Alhaji Auwalu Ado Bayero a Matsayin Sadaukin Kano da Alhaji Ado Ado Bayero a Matsayin Cigarin Kano.

Shugabancin majalisa: Abubuwan da aka tattauna tsakanin Tinubu, Akpabio da Barau Jibri

Mai martaba Sarkin Kano ya horesu dasu Sanya halayyar magabatansu na yin koyi da kyawawan halaye wadanda sukabhadar da Juriya da hakuri da amana da tausayawa talakawa.

 

Yace su dauki halayyar magabata ta mika dukkan al’amuransu ga Allah tare da yin biyayya ga wadanda suka tarar a cikin tsarin hakimci da kuma yin da’a kamar yadda suka taso sukaga anayi Kasancewarsu dukkanninsu yan gidan sarautar Kano ne.

 

Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci hakiman da aka nada su zamo jakadu nagari a duk inda suka samu kansu tareda gudanar da aikinsu da gaskiya da amana tareda Sanya tsoron Allah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...