Daga Halima Musa Sabaru
Kasar Saudiyya ta kammala shirin fara duban watan sallah a daidai lokacin da al’ummar Musulmi suka ɗauki azumi na 29.
Sashin Shafin Masallacin Harami na Makka da Madinah ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa daga yau Alhamis za a fara duban watan na Shawwal.
Rarara ya Magantu kan korar yan sandan dake bashi kariya
An kuma girke manyan na’urori domin aikin fara duban watan na Shawwal.
A Najeriya ma Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bukaci al’umma su fara duban jaririn watan Shawwal daga yau Alhamis 29 ga watan Ramadan.