Rarara ya Magantu kan korar yan sandan dake bashi kariya

Date:

Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman

 

Shahararren mawakin nan Dauda kahutu Rarara ya bayyana cewa ya dauki nauyin cigaba da biyan albashin yan sandan nan guda uku suke bashi kariya, wanda rundunar yan sanda ta kasa ta koresu daga aikin sakamakon karya ƙa’idar aiki.

 

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Rundunar yan sanda ta kasa ta kori wasu yan Sanda guda uku wanda suke rakiyar mawaki Rarara, saboda harba bindiga da sukai ba bisa ƙa’ida ba, lokacin da suka raka Rarara garin su na kahutu ,Inda yayi rabon kayan abinchin.

Yadda sabon dan majalisar tarayya na Fagge MB Shehu yaki gaisawa da jami’ar INEC

Rarara ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da manema labarai a kano.

An kori ‘yan sandan da ke yi wa mawaki Rarara rakiya

Rarara wanda shi ne shugaban kungiyar 13+13 yace bayan sallamar yan sandan daga aiki sun sanar da shi , shi yasa ya tambaye su adadin abun da ake biyansu, matsayin albashin su kuma nan taka yayi alkawarin cigaba da biyansu, har lokacin da za’a Maida su bakin aikin su.

 

” Sun fadamin su shigar da Kara kuma na ce su cigaba da neman hakkinsu, Amma dai na gaya musu idan babana ya zo , to babu shakka za’a Mayar da su bakin aikin su, kuma kowa yasan baba nan zai zo mulkin Nigeria nan bada jimawa ba”. Inji Rarara

” An kona min gida, an koma ofishin na an Kuma Kona min plaza, Kuma an san akwai masu neman illata ni ko ma rayuwa ta baki daya, amma duk da haka aka dauki wannan matakin akan Masu bani tsaro, to ba komai nan bada jimawa ba baban zai zo, duk da na nemi alfarma amma aki ayi min”. Inji Dauda kahutu Rarara

Shugaban kungiyar ta 13+13 ya sanya bidiyon wasu jami’an yan sanda suna harba bindigu sama, Inda ya roki rundunar da kada ta kore su saboda laifin da sukai yayi dai-dai da irin abun masu tsaronsa suka yi, Inda yace kada a koresu daga aiki ne saboda su basu san shi ba ballantana idan baban shi ya zo mulki ya roka musu alfarma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...