Yanzu-Yanzu: Sanata Shehu Sani ya fice daga jam’iyyar PRP

Date:

Daga Juwairiya Adam Mai gida


 Tsohon sanatan kaduna ta tsakiya ya gabatar da takardar ficewa daga jam’iyar PRP nan take.


 Sanata Shehu Sani, wanda ya koma jam’iyyar a watan Oktoba na shekarar 2018, ya bayyana hakan ne a wata wasika mai dauke da kwanan wata 9 ga watan Yulin sannan ya aiketa ga shugaban jam’iyyar ta PRP a shiyya ta shida, Tudun Wada, Kaduna.


 “Ina son sanar da ku a hukumance game da shawarar da na yanke na ficewa daga Jam’iyyar PRP.  Wannan sanarwar ta fara aiki ne daga yau, ”ya ce a cikin kwafin wasikar da ya aikewa Manema labarai.


 Ba tare da ya bayyana dalilan ficewar tasa ba da Kuma Inda Zai koma, Shehu Sani ya kara da cewa “Ina fatan za mu ci gaba da hulda da gwagwarmaya, da kuma dabbaka akidunmu na gaskiya”.


 Wasu rahotanni a kafafen sada zumunta a baya sun ce Sanata Shehu Sani ya kasance yana tattaunawa da jam’iyyar ta PDP a jihar da niyyar Zai koma Cikin ta.


 Majiyar Kadaura24 tayi kokarin Jin ta bakin shugaban jam’iyyar ta PRP na kasa, Falalu Bello, abun da Zai ce Kan ficewar Shehu Sani Amma hakan bata yiwuba. 


 Sanata Sani ya koma PRP ne kwanaki bayan ya fice daga APC, wadda ya lashe zaben Sanatan Kaduna ta Tsakiya a ranar 28 ga Maris din 2015 da ita.

79 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Babbar Sallah: Gwamnatin Kano ta sanar da ranar rufe makarantu a jihar

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da...

Ban San Taulaci ba Sai da na Zama Sarkin Kano – Sarki Sanusi II

Daga Isa Ahmad Getso Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi...

Iftila:I: Gwamnatin Kano ta Aiyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin...

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...