Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nada Hon. Surajo Umar Wudil a matsayin Babban Mataimaki na musamman ga gwamnan kano akan harkokin kafafen yada labarai Radio da talabijin.
” An baka wanann mukami ne saboda sadaukarwar da Kuma gogewar da kake da ita a fannin Siyasa da yada labarai , Muna fata za ka mai da hankali wajen sauke nauyin da aka dora maka don ciyar da gwamnatin gwamna Ganduje gaba”. Inji Sanarwar
Fatawa: Ya halatta ayi zakkar fidda kai da Taliya Kuskus ko Indomie – Mal Ibrahim Khalil
A wata wasika Mai dauke da kwanan watan ranar 17 ga watan Afirilu 2023, wacce babbar sakatariyar ofishin Sakataren gwamnatin jihar kano bilkisu Shehu maimota ta sanyawa hannu, tace nadin nasa ya fara aiki ne tun a watan satumba na shekarar 2023 da ya gabata.
Gwamnan ya taya Surajo Umar Wudil murnar samun wannan mukami tare da umartar shi da ya ba da gudunmawa wajen ciyar da jihar kano gaba ta kowacce fuska.