Fintiri ya lashe zaben gwamnan jihar Adamawa

Date:

Daga Maryam Ibrahim Muhammad

Hukumar zaɓe a Najeriya ta sanar da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaɓen jihar Adamawa, wanda ya ƙare cikin taƙaddama.

Jami’in sanar da sakamakon zaɓen gwamna na Adamawa, Farfesa Mohammed Mele ya ce Ahmadu Fintiri ya yi nasarar lashe zaɓen ne da ƙuri’a, 430, 861.

Da dumi-dumi : INEC ta bayyana Matsayarta kan Zaben Gwamnan Jihar Adamawa

Gwamnan mai ci ya samu nasara a kan babbar abokiyar fafatawarsa Aisha Ɗahiru Binani wadda ta samu ƙuri’a, 398, 788.

Fatawa: Ya halatta ayi zakkar fidda kai da Taliya Kuskus ko Indomie – Mal Ibrahim Khalil

Wannan nasara ta bai wa Fintiri ikon ci gaba da mulkin jihar Adamawa a wa’adi na biyu.Da yammacin Talata ne, jami’in sanar da sakamako, Farfesa Mohammed Mele cikin rakiyar wasu manyan jami’an INEC na ƙasa, ya isa zauren karɓar sakamako da ke Yola, inda ya ci gaba da aikin tattara sakamakon ƙananan hukumomin da suka rage.

 

A ranar 15 ga watan Afrilu ne, hukumar zaɓe ta gudanar da cikon zaɓen cikin wasu rumfuna da ke faɗin ƙananan hukumomin jihar 20.

 

An sake kaɗa ƙuri’u ne a tashoshin zaɓe 69.

Sakamakon zaɓen da aka ƙarasa ya nuna cewa ‘yar takarar jam’iyyar APC, Aisha Binani ta samu ƙuri’a 6,513, yayin da Gwamna Fintiri na PDP ya samu 9,337.

Zaɓen dai ya gamu da taƙaddama bayan kwamishinan zaɓe na jihar Adamawa Hudu Ari ya sanar da Aisha Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen ba tare da ya fayyace sakamakon kowacce jam’iyya dalla-dalla ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya tura tawaga mai karfi wajen Abba Ganduje

Daga Rahama Umar Kwaru   Babban Daraktan Hukumar Samar da Wutar...

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...