Fatawa: Ya halatta ayi zakkar fidda kai da Taliya Kuskus ko Indomie – Mal Ibrahim Khalil

Date:

Daga Fatima Kabir Labaran

 

Shugaban majalisar malaman jihar kano Mal Ibrahim Khalil ya bayyana cewa ya halatta mutum ya yi zakkar fidda Kai da nau’in Abinchi kamar su taliya ko Kuskus ko Kuma Indomie ma .

 

” Ana yin zakka fidda kai ne da abun da za’a iya ci ranar Sallah, don haka ya halatta a bada ita da wadancan kayan Abinchi, ba ku rika baiwa mutane dawa ko gero ba, domin babu wanda zai ci dawa ko gero a ranar Sallah”.

Malam Ibrahim Khalil ya bayyana hakan ne cikin wata tattauna da yayi ta wayar tangaraho da gidan Radio express dake kano.

Yace a baya ana bada gero da dawa ne lokacin zakkar fidda Kai saboda Malam bahaushe a wancan lokacin bashi da shinkafa taliya kuskus da makaroni, yace ko ma akwai su to ba kowa ne zai iya siya ba, amma Yanzu dukkanin su sun ma fi saukin sarrafawa .

” Hikimar zakkar ita ce don a samawa talaka abun da zai ci a ranar Sallah don haka duk abun da aka bayan a cikin wadanda abinchin yayi, kuma za’a iya bada kudi ma Kuma wannan ma shi yafi saboda wanda aka baiwa zai iya siyan abun da yake bukata”. Inji Mal Ibrahim Khalil

 

Da yake baiwa yadda za’a fitar da zakkar da taliya kuskus da makaroni ko Indomie, malamin yace kamar taliya kuskus da makaroni za’ a iya bada leda dai-dai a matsayin kowanne mudannabi, ita kuma Indomie tunda karama ce za’a iya ba da manya guda biyu ga kowanne mutan guda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...