Daga Ibrahim Sani Gama
Masarautar kano ta sha alwashin tallafawa kungiyar matuka motocin Akorikura ta( NURTW) reshen railway dake nan kano, cikakkiyar gudunmawar da ta kamata domin ciyar da harkokin sufuri gaba.
Hakimin karamar hukumar fagge Alh Muhamud Ado Bayero Turakin kano ne ya bayyana haka a lokacin da kungiyar ta kai masa ziyara domin taya shi murna tare da bashi lambar girmamawa,bisa daga likkafar da Sarkin Kano ya yi.
Muhamud Ado Bayero, yace fadarsa a shirye take wajen tallafawa kungiyar matuka motocin Akorikura ta railway, wajen inganta sana’arsu yadda ta kamata, duba da irin jajircewar da yan kungiyar su ke da ita ta fannin samarwa matasa ayyukan dogaro da kai.
FCE Bichi na daf da durkushewa, saboda matsalolin da suka yi yawa a makarantar – Dr. Hussaini Peni
Turakin kanon, ya kuma hori yan kungiyar da su kasance masu bin dokokin tuki da kaucewa tukin ganganci a yayin gudanar da ayyukansu musamman, idan suka hau manyan tituna.
” kofarmu a bude take ga duk wata bukata da kungiyar ku zata zo da ita don ciyar da harkokin sufuri da kare martabar masarautar kano da tallafawa matasan jihar kano ta fannoni da dama”.
A jawabinsa shugaban kungiyar matuka motocin Akorikura ta kasa reshen railway dake nan kano, Abubakar Daniya Bala, yace sun kawo zayarar ne domin taya hakimin murna bisa karin girman daya samu daga Tafidan kano zuwa Turakin kano, mai martaba sarkin kano Alh.Aminu Ado Bayero ya tabbatar.
Daniya Bala ya kuma ce, kungiyar tana bukatar fadar hakimin karamar hukumar Fagge, da ta shigewa kungiyar matuka motocin Akorikura gaba domin samar mata gurin tsayawa na din din din karkashin Gwamnati.
Shugaban kungiyar yace, duba da gudunmawar da fadar hakimin take baiwa kungiyar matuka motocin Akorikura ta kasa reshen railway dake nan kano, ya karawa kungiyar kaimi wajen bashi lambar girmamawa da taya shi murna bisa Karin matsayin daya samu daga masarautar kano.
Ya jaddada kudirin kungiyar matuka motocin Akorikura ta kasa reshen jihar kano dake railway, wajen baiwa masarautar kano hadin kan daya kamata domin kare martabar masarautar kano da fadar maigirma Hakimin karamar hukumar fagge.