Daga Abubakar Lawan Bichi
Kungiyar Mallaman Kwaleji Ilimi ta Tarraya dake Bichi wato COASU ta shiga yaji aiki sai baba ta gani, Sakamakon lalacer abubuwan a Makarantar da rashin iya gudanar shugabanci na shugaban Makarantar Professor Bashir Muhammad Fagge.
Shugaban Kungiyar ta COASU DR. Hussaini Yahaya Peni da Sakataren Moji Kenneth Terngu Suka bayyana haka yayi Ganawarsu ga manema labarai a Cibiyar Kungiyar Yan Jaridu dake nan Kano.
Dr. Hussaini Yahaya Peni ya ce makarantar ta dauki hanyar durkushewa saboda dakunan Gwajegwaje Kimiya da Fasaha na Makarantar sun lalace, basa yin aiki sakamakon rashin kulawa daga hukumar Makarantar ta FCE Bichi.
Zaɓen Gwamnan Kano: APC ta roki kotun sauraren kararrakin Zabe har abubuwa guda 5
Dr. Peni ya kuma fargabarsa na amkuwar aiyukan ta’addanci sakamakon rashin Tsaro a Makaranta Saboda rashin kulawa na Shugabanci Makarantar na yanzu.
Dr. Hussaini Yahaya Peni ya kara da cewar Ma’ikata a makaranta sun zama koma bayan sakamakon rashin biyansu hakokinsu, rashin biyan Kudade taimakekeniyar Lafiya, da rashin saka kudade da ake yankewar Ma’ikatar na wata-wata zuwa Asusu na MultiPurpose Cooperative da kuma dukkanin wasu H?hakkokin Ma’ikata.
Akwai rashin Samar da kayan karatu, lalacewar dakunan Kwanan dalibai, ajujuwan karatu da kuma rashin sakar kudade da Asusun dake tallafawa ilimi na Kasa wato TETfund ya Samar aka tsare-tsare cigaban ilimi a Makarantar Kamar horal da dalibai Sani Makamar aiki teaching practice, Samar litartafai da kuma kari sanin makamar aiki ga Mallamai.
Dr Hussaini Yahaya Peni yace basu da wata mafitar Sai dai su shiga yaji aiki sai baba ta gani domin ceto makarantar daga durkushewa.