DAGA MUKHTAR YAKUBU
ƊAYA daga cikin manyan mawaƙa mata a Kannywood, Fati Kawo, ta bayyana cewa cutar da shugabannin sabuwar ƙungiyar su ka kitsa ne ta haifar da rikici a cikin ƙungiyar.
A fusace, Fati ta faɗa wa Majiyar Focus News Hausa, mujallar Fim cewa: “Dalilin da ya sa Fa’iza Badawa ta kafa ƙungiyar, saboda ran ta ya ɓaci ta yi burin kafa ƙungiya saboda mu mu ne mawaƙa amma sai mu ga maza su na ɗauko mata ‘yan fim su na ɗorawa a kan waƙoƙin mu su na fita su na samun kuɗi,don haka mu me ya sa ba za su saka mu ba? Kuma me ya sa idan an fita an samo kuɗin mu ba za a ba mu haƙƙin mu ba?.
Zaɓen Gwamnan Kano: APC ta roki kotun sauraren kararrakin Zabe har abubuwa guda 5
“Mawaƙa maza sun mayar da mu saniyar tatsa, don haka mu ka yi yunƙurin kafa tamu ƙungiyar tunda mu ma mun iya waƙar nan, abin da su ka yi mu ma za mu iya. Sai Fa’iza Badawa ta buɗe guruf ta ɗauko duk wata mawaƙiya ta saka ta a ciki. Kuma daga nan aka fara zuwa wajen mawaƙa manya maza su na ba mu shawarwari na yadda za mu riƙe ƙungiyar. Har Sadiq Zazzaɓi ya ke ba mu shawarar cewa duk wata mawaƙiya da ta ke Kano, duk ƙanƙantar ta a saka ta a ƙungiyar, sannan sai an yi haƙuri idan maganar kuɗi ta zo a kawar da kai saboda sun yi ƙungiyoyi da dama sun samu matsaloli. Don haka duk abubuwan da su ka faru sai da aka ba da shawarwari, amma ba a ɗauka ba.”
Rashin wuta: ‘Yan KEDCO ya kamata ku nemi aljannar ku a wanann wata na Ramada – Falakin Shinkafi
Ta ci gaba da cewa, “Mu na cikin wannan sai mu ka ga cewa ita ƙungiyar mu sabuwa ce, ba ta da kuɗi, kuma mu ma ba kuɗi ne a wajen mu ba, don haka ni Fati Kawo sai na ba da shawarar ya kamata mu je wajen manyan mu tunda ga su Abdul Amart, mu je mu nemi shawara da kuma buƙatar taimako. Don ko rajista ba mu yi mata ba, kuma ba mu da ofishin ƙungiyar, ba mu da komai.
“Sai Ibrahim Ibrahim ya yi mana hanya mu ka je mu ka samu Abdul Amart. Bayan ya ba mu shawarwari, ya ɗauko miliyan ɗaya ya ba mu. Sannan kuma ya yi mana alƙawari zai yi mana rajista ta C.A.C.
“Sai aka zo aka cire wa ƙungiyar wani abu, sai aka raba kuɗi har waɗanda ba su je ba ma sai da aka ba su.
“To kuma tun daga nan ƙananan maganganu su ka fara tashi a wajen waɗanda su ba sa cikin ƙungiyar amma an neme su an ba su kuɗin. Don haka sai mu ka ci gaba mu na faɗi-tashi, yau mu ne a zauna taro gidan waccan gobe a tafi gidan Zoo. Haka dai aka yi ta yi.
“To, shi ne fa na kawo yadda za a yi a samu wani abu, tunda na ga ina da hanyar da za a samu kuɗi a Gombe, kuma na yi magana aka ba da damar a yi aikin nan har aka yi, aka yi gwagwarmaya aka buɗa, wani abu ma ba zai faɗu ba, aka yi aikin nan.
“To, da man an ce ƙa’idar ƙungiyar duk abin da aka yi aiki aka samo, in mutum ya yi hanyar da aka samu, za a ba shi kaso goma, kuma za a raba kuɗi da shi. To, da aka zo rabo sai aka ce ba za a raba da ni ba sai dai a ba ni kaso goma. Tun daga nan aka fara samun matsala, ya zama ko na kira su a waya ba sa ɗagawa. Kuma da man tun a kaso na biyu na kuɗin aikin haka su ka yi rabo babu ni, saboda wai ni ban ɗora murya ta ba, sai aka ce idan an je neman kuɗi na gaba za a cire mani kason, to amma dai an tsaya an cire mini kason nawa kuma aka ba ni 250,000 a ciki. Wannan shi ne a cikin miliyan tara, na samu miliyan ɗaya da ƙyar!
“To wannan ne ya zama abin magana ake cewa ba ni da mutunci, sai abin ya dawo zagi, an ɗauki miliyan ɗaya an ba ni, an ajiye wa ƙungiyar miliyan ɗaya, an bai wa ‘yan Gidan Gwamnati miliyan ɗaya. Shi ne aka zo aka yi wannan kashe-mu-raba, har wadda ta ɗora waƙa murya ɗaya aka ɗauki manyan kuɗi aka ba ta, amma wadda ta yi waƙa huɗu biyar aka ɗauki dubu ɗari biyu aka ba ta.
“Don haka ina zaman lafiya zai fara tun daga nan? Sai rashin mutunci. Da ka yi magana sai a hawo kan ka, don kaza-kazan ka, waye waye.
“Don haka babu wani mai hankali da zai ɗauki irin waɗannan abubuwan.
“Sai daga baya aka zo aka ce a ware rana da za a zo a zauna, don a san nawa aka samu kuma nawa aka kashe, nawa ya rage, kuma nawa aka ajiye wa ƙungiyar. To har yau abin da ba a yi ba kenan. Su na nan sun tasa kuɗi a gaba sun cinye.
“Don haka, mu tunda abin ya zo da rashin mutunci har ana maganar ai su na da ‘ya’yan shegun da za su iya cin kaza-kazar mu, shi ya sa mu ma mu ka rabu da su mu ka bar su. In har zalunci ya na ɗorewa, to ya ɗore a wajen su mu gani.”