Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Jam’iyyar APC reshen Kano ta shigar da kara a gaban kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano, tana kalubalantar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) kan ayyana Abba Kabir Yusuf na NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a jihar a ranar 18 ga watan Maris, 2023.
A wata kara mai juzu’i 5 da ta shigar da yammacin ranar Lahadin data gabata, mai shigar da kara, (APC) na zargin cewa, Abba Kabir Yusuf bai cancanta ya tsaya takara ba, saboda ba ya cikin jerin sunayen mambobin NNPP da aka aika wa hukumar INEC.
Tinubu ba ya bukatar kaso 25% na kuri’un FCT domin ya ci zaben Shugaban Kasa- INEC
Jam’iyyar APC ta kuma yi zargin cewa NNPP ba ta ci zabe da mafi yawan kuri’u na halal ba, tana mai cewa wasu kuri’un da aka kada musu na Jabu ne, kuma idan aka cire su daga kuri’un da NNPPn ta samu, APC ce za ta samu kuri’u ma fi yawa da aka kada.
Rashin wuta: Yan KEDCO ya kamata ku nemi aljannar ku a wanann wata na Ramada – Falakin Shinkafi
Majiyar Kadaura24 Justice Watch News ta rawaito cewa, a cikin karar, APC ta kuma yi zargin cewa Kwamishinan Zabe na Jihar Kano (REC) ya yi kuskure kan ayyana Abba Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben, inda ta ce tazarar kuri’un da aka samu bai wuce kuri’un da aka soke ba, kamar yadda ta bayyana cewa ya kamata a ce zaben bai kammala ba.
Mai shigar da kara tana neman kotun da ta bayyana cewa NNPP ba ta da dan takara saboda Abba Kabir Yusuf baya cikin rajistar masu kada kuri’a da suka mika wa INEC a lokacin zabe, inda ya bukaci kotu ta bayyana Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben, ko kuma ta bayyana APC a matsayin wadda ta lashe zaben ta samu mafi yawan kuri’un da aka kada idan an cire kuri’un bogi da aka kadawa NNPP.
Hakazalika mai shigar da kara ta roki ko Kotun a madadin ta bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba, yana mai zargin cewa tazarar ba takai adadin kuri’un da aka soke ba.
Jam’iyyar APC dai ta yi karar Abba Kabiru Yusuf da jam’iyyar NNPP da Kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC.
Bisa ka’idar kotun, wadanda ake kara suna da kwanaki 21 da za su mayar da martani akan bukatar bayan da kotuna ta yi aiki a kansu.