Daga Rukayya Abdullahi Maida
Amb. Dr. Yunusa Yusuf Hamza Falakin Shinkafi ya bukaci kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na Kedco da ya ɗauki matakan da suka dace wajen magance matsalar wutar lantarki data addabi jihohin Kano Jigawa da katsina a wannan lokaci na azumin watan Ramadan.
“Rashin wutar lantarki yasa al’ummar jihohin Kano Katsina da Jigawa cikin mawuyacin hali a wannan watan na Ramadan, don haka akwai bukatar Kedco su dauki matasakin da ya dace ” a cewar Falakin Shinkafi
Amb. Yunusa Yusuf ya bayyana hakan ne yayin ganarwa da wakilin Kadaura24 a yammacin ranar talatar nan.
Ramadan: Mutune sama da miliyan 1 ne suka je Ibadar Umara Saudiyya
“Tun lokacin da aka fara ibadar azumin watan Ramadan, mutanen wadancan jihohi suka shiga mawuyacin hali sakamakon rashin wutar lantarki, wanda hakan bai dace ba idan aka duba da muhimmancin watan”.
Likitoci a Najeriya sun soki sabon ƙudurin Majalisar wakila ta ƙasa
” Ana zargin yan Kedcon suna sayar da wutar ne ga masu kankara wanda wannan ba dai-dai bane, wata ne aka ake bukatar a kwaitatawa al’umma , Amma abun mamaki suna musgunawa mutane saboda kin bada wutar lantarki wadda da ita ce ake dan samun abun Sanya idan an Sha ruwa”. Inji Amb. Yunusa Yusuf Hamza
Falakin Shinkafi ya yi kira ga yan Kedcon da su yi kokarin Neman aljannar su ta hanyar kyautatawa Masu Azumi a wanann watan mai tarin falala na Ramadana