Daga Rahama Umar Kwaru
Ministan ma’aikatar aikin Hajji da Umara ta ƙasar saudiyya Dr. Tawfiq Al-Rabiah ya bayyana cewa biranen Makka da Madina sun samu masu ziyarar ibada daga ƙasashen waje masu yawan gaske a wannan wata.
Dr. Tawfiq ya ce ya zuwa yanzu an samu masu ziyarar ibada miliyan 1.3 a manyan biranen ƙasar biyu.
Likitoci a Najeriya sun soki sabon ƙudurin Majalisar wakila ta ƙasa
Ministan ya ce ana samun ci gaba a harkokin sufurin masu ziyarar ibada tare da inganta harkokin ibada musamman a cikin masallatai biyu masu alfarma a ƙasar.
‘Yan mata sama da dubu 42 ne suka daina zuwa makaranta saboda sun yin ciki – Rahoto
”Muna bakin ƙoƙarinmu wajen samar da kyakkyawan yanayi domin jin daɗin mahajjata a biranen Makka da Madina”, in ji shi.
”A kodayaushe muna kan inganta biranen biyu, kuma akwai wuraren tarihi sama da 100 tsakanin biranen biyu”, a cewarsa.
Ministan ya ce ana sa ran sama da mutune miliyan biyu ne za su yi aikin hajjin bana a wannan shekara.