Hukumar jin dadin alhazai ta Kano ta sanar da dalilan da suka sa kudin hajjin bana ya yi tashin gwaron zabi

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Hukumar Jin dadin alhazai ta jihar kano tace dalilai ne Masu yawa suka sa kudin kujerar aikin hajjin bana ta yi tashin gwaron zabi a Nigeria da duniya baki daya.

 

Sakataren zartarwa na hukumar Malam Muhammad Abba Danbatta ne ya bayyana hakan Yayin da ya gana da manema labarai bayan Jim kadan bayan Nahcon ta sanar da kudin aikin hajjin bana.

 

Danbatta yace tashin da dalar Amurka ta yi na daya daga cikin dalilin tashin kudin, sai Kuma batu sake ginin masaukan alhazai a kasa mai tsarki da hukumomin kasar sake yi, don inganta Jin dadi da walwalar alhazai bakin Allah.

Kammala zaben 2023: Abba Gida-gida ya baiwa shugabannin kananan hukumomin Kano shawara

” Akwai Kuma batun tashin fara shin dajunkunan da alhazai suke amfani da su manya da kanana dukkanin su farashin su ya tashi ba kamar yadda suke a bara ba, shi ma uniform da ake baiwa alhazai ya tashi Inda a baya muke basu kala biyu akan Naira dubu 6, Amma a bana zai tashi ne akan naira dubu 8, sannan shi kansa tikitin jirgin sama ya tashi saboda tsadar man jirgi da dai sauransu”. Inji Muhd Abba Danbatta

Alhassan Ado Doguwa ya yi Nasara, Kotu ta bada umarnin karasa zaben Tudun Wada da Doguwa

Sakataren zartarwar ya kuma ce maniyata aikin hajjin bana zasu biya kuɗin kujera Naira Miliyan 2 da dubu dari tara da goma Sha tara, Inda yayi kira ga duk wadanda basu cika kudin ba da su hanzarta cikawa kafin ranar 21 ga wannan wata na afirilu domin ita ce ranar da za’a rufe karbar kuɗin kujerar aikin hajji a kasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Ganduje ya yi murabus daga shugaban jam’iyyar APC na kasa

Daga Abdullahi Shu Shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Umar...

Murtala Sule Garo Ya Taya Al’ummar Musulmi Barka da Shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1447AH

    Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano, Alhaji Murtala...

Tinubu zai mayar da Fubara kan kujera gwamnan Rivers amma ya gindaya masa sharadi- Rahoto

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da mayar...

Yadda Makarantar JSS Unguwa uku dake K/H Tarauni ta Zama mafakar shaye-shaye da yan daba

Daga Mubina Ahmad Galadanchi Wasu daga cikin al'ummar unguwar unguwa...