Kungiyar RATTAWU ta taya Abba Gida-gida Murnar lashe zaɓen gwamnan Kano

Date:

Daga Maryam Muhd Ibrahim

 

Kungiyar ma’aikatan Radio da talabijin da wasan kwaiwayo ta kasa reshen jihar kano ta taya sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar kano Engr. Abba Kabir Yusuf murnar lashe zaben gwamnan jihar kano.

 

Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Shugaban kungiyar na jihar kano Babangida Mamuda Biyamusu Kuma ya aikowa kadaura24.

 

Abba Gida-gida ya shawarci  masu gine-gine a wararen Gwamnatin kano da su dakata

Sanarwar tace tana taya Abba Gida-gida Murnar a madadin kafafen yada labarai dake kano,tare da fatan zai samar da kyakyawar dangantaka tsakanin sa da kafafen yada labaran don samun nasarar gwamnatin sa.

Ina godiya ga yan jaridu bisa hadin kan da suka ba ni  inji mai magana da yawun Ganduje Abba Anwar

 

” Babu Shakka kasancewar ka gwamnan jihar kano a wannan lokaci zai baiwa jihar damar amfana daga basira da kwarewar da kake da ita wadda ka nuna ta lokacin da ka rike kwamishinan aiyukan na jihar kano, lallai Kano zata sami cigaba ta fannoni daban-daban”. Inji sanarwar

Yace kungiyar taza yi duk mai yiyuwa wajen ganin ta baiwa sabon zaɓaɓɓen gwamnan kano hadin kai da goyon baya don ganin ya Sami nasara a mulkin da zai yi was jihar kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...