Daga Abubakar Sa’id Sulaiman
Zababben Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, na shawartar dukkanin masu yin gine-gine a filayen gwamnati da suka hadar da makarantu, kasuwanni, filayen wasanni da kuma badala da su dakata da wadannan aiyuka.
Emgr. Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan cikin ta cikin wata sanarwa da Babban Sakataren yada labaran sa Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24 a daren jiya Alhamis.
- ” Mun ɗauki wannan matakin ne saboda bukatar al’umma, Amma kuma duk wanda ya cigaba da yin gini a Inda aka hana to duk abun da ya faru ya kuka da kan shi”. A cewar Zaɓaɓɓen gwamnan kano
Idan ba a manta ba jam’iyyar NNPP da shi kan sa zaɓaɓɓen gwamnan ya Sha maganar cewa ba za su lamunci gine-gine a warare mallakin gwamnatin jihar kano ba , musamman idan suka zabo mulkin kano.
Sanarwar dai bata fayyace matakin da zaɓaɓɓen gwamnan zai ɗauka ba , akan Masu yin irin wadancan gine-gine, Amma mutane suna ta hasashen akwai yiwuwar a rushe gine-gine saboda anyi su ba bisa ƙa’ida ba.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito ana zargin gwamnati Mai barin gado ba sayar da filayen ga yan kasuwa da sauran al’umma, wanda gwamnatin ta ce ta yi hakan ne domin kara bunkasa birnin kano da Kuma kasuwanci a jihar.