DSS ta ce ta gano makarkashiyar kafa gwamnatin rikon kwarya a Nigeria

Date:

Daga Halima Musa Sabaru

 

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya ta ce ta shaida wasu jiga-jigai a wata maƙarƙashiya ake kitsawa don kafa gwamnatin riƙon ƙwarya a Nigeria.

 

Hukumar ta ce maƙarƙashiyar, wanda wasu ke izawa ba kawai abu ne da ya saɓa wa doka ba, wani ƙoƙarin masu jamhuru ne na kifar da tsarin mulkin Najeriya da kuma jefa ƙasar cikin wani rikici da za a iya kaucewa.

 

Yanzu-Yanzu: Nasiru Gawuna ya taya Abba Gida-gida Murnar lashe zaɓen gwamnan Kano

Ta ce tunanin kafa gwamnatin riƙon ƙwarya, abu ne da ba za a amince da shi ba a tsarin dimokraɗiyya da kuma zaman lafiyar al’ummar ƙasar.

 

A saƙon da ta wallafa a shafinta na Tuwita ɗauke da sa hannun jami’in yaɗa labaran hukumar, Peter Afunanya, DSS ta ce tun bayan zaɓukan ƙasar da aka kammala cikin kwanciyar hankali, ake ta raɗe-raɗin kafa gwamnatin riƙo.

INEC ta baiwa Abba Gida-gida Shaidar lashe zaben gwamnan Kano

Sai dai DSS ba ta fito kai tsaye ta ce ga ‘yan siyasar da take zargi da shirya wannan maƙarƙashiya ba.

Ta dai ce masu kitsa makircin, a jerin tarukan da suke yi, suna auna batutuwa da dama a ciki har da yadda za su ɗauki nauyin zanga-zanga maras iyaka a manyan birane ta yadda daga bisani za a ayyana dokar ta-ɓaci.

Wani abin kuma shi ne, su samu umarnin kotu don hana rantsar da sabbin shugabanni da ƴan majalisa a matakin tarayya da jihohi.

Hukumar DSS dai ta bayyana goyon bayanta ga Shugaba Muhammadu Buhari a ƙudurinsa na tabbatar da ganin an miƙa mulki ba tare da wani tashin hankali ba kuma za ta yi aiki tuƙuru don ganin tabbatuwar hakan.

Ta kuma goyi bayan kwamitocin miƙa mulki da shugaban ƙasar ya kafa da kuma waɗanda aka kafa a jihohi.

Hukumar ta ƙara da cewa za ta yi aiki da sauran hukumomin tabbatar da tsaro domin ganin an yi bikin miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

 

DSS ta kuma gargaɗi masu shirin daƙile dimokraɗiyyar ƙasar su janye ƙudurinsu ta kuma buƙaci hukumomi a ɓangaren shari’a da kafofin labarai da ƙungiyoyin farar hula su zama masu lura da taka tsantsan don kada a yi amfani da su wajen tayar da fitina da ruguza zaman lafiyar ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...