Daga Abdulrashid B Imam
Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta a Najeriya ta miƙa wa Abba Kabir Yusuf shaidar lashe zaɓen gwamnan jihar Kano.
An dai jima ana jiran wannan rana kasancewar yan jam’iyyar APC sun shigar da kake kan yadda aka bayyana sakamakon zaben gwamnan na jihar kano, Inda sukai zargin akwai kura-kurai.
Ga hotunan yadda taron bada Shaidar ya kasancewa:
Abba Kabir, wanda ya yi nasara zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, ya samu ƙuri’u 1,019,602, yayin da Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC ya samu ƙuri’u 890,705.