Sabon zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tafi Turai domin ya hutu, daga can kuma zai nufi Saudiyya domin aikin Umrah.
Kakakin Tinubun Tunde Rahman ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba.
A sanarwar kakakin ya ce, Tinubun ya fita ne domin ya je ya huta daga gajiyar kakar yakin neman zabe da kuma zaben sannan kuma ya tsara shirinsa na karbar mulki kafin ranar kaddamarwarsa ta 29 ga watan Mayu na shekarar nan ta 2023.
Tunde ya ce zaɓaɓɓen shugaban ya tashi daga filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Ikeja, a Lagos zuwa Turai a jiya Talata da daddare, inda zai je Paris da kuma London domin ya huta, sannan kuma ya wuce Saudiyya domin Umrah da azumin Ramadan da za a fara a gobe Alhamis.