Dilolin Siminti da Masu Siya Sun koka da tsadarsa a Kano

Date:

Daga Zubairu Gambo Sagagi

Diloli da kwastomomin siminti a jihar Kano sun nuna damuwa da rashin gamsuwa game da karin farashin siminti da kamfanin BUA Cement Plc ya yi.

Rahotanni nuna cewa kamfanin ya kara farashin simintin Kamfanin da da Naira dari biyu Inda ya tashi daga N2,800 zuwa N3,000 kowanne buhu, lamarin da ya haifar da fargaba a zukatan al’ummar jihar nan.

A cikin wasu sanarwa da Kamfanin na BUA ya fitar tsakanin 24 ga Afrilu zuwa 18 ga Yunin wannan shekarar, ya karyata batun karin farashin simintin da N300 a kan kowanne buhu.

Rahotanni na nuni da cewa kamfanin ya riga ya kara N200 akan kowanne buhun siminti ga dilolinsa, wanda hakan ya haifar da fargabar cewa farashin kayan zai yi tashin gwauron zabo daga N3,600 zuwa N3, 800.

Wani bincike da aka gudanar a Kano a ranar Larabar nan ya nuna cewa dukkan dilolin siminti da masu sayansa suna cikin fargabar karin farashin zai kara tu’azzara halin matsin tattalin arzikin da ake fama da shi.

Wani dilan siminti a Kano, Musa Shehu, wanda ke sayar da siminti a Sallari Blocks, ya ce ya ji labarin karin farashin kayan amma har yanzu ba a Fara sayar dashi a Haka ba.

A cewarsa, har yanzu ana siyar da buhun siminti a kan N3,550 ko kuma N3,600, ya nuna fargabar cewa karin zai yi Fara aiki nan ba da jimawa ba.

Shehu ya bayyana cewa karin farashin siminti na BUA da N200 hakika zai haifar da matsi ga masu siye da siyarwa baki daya, yana mai cewa yanzu kayan suna nan amma idan suka kare, tabbas karin farashin zai fara aiki.

“Farashin yanzu ya shafi manyan diloli ne,amma tabbata zai sauko zuwa ga Kananan ‘yan kasuwa. Saboda haka muna kira ga shuwagabannin kamfanin BUA da su duba wannan shawarar kuma su sauya farashin saboda zai shafe mu, tunda kwastomomi za su daina sayen kayan daga gare mu, “a cewar sa

Wani dilan, Auwalu Umar, ya ce a kowanne lokaci na damina ana samun saukin simintin musamman a arewacin Najeriya, yana mai korafin cewa bai kamata kamfanin siminti na BUA ya kara farashin ba sakamakon matsin tattalin arziki da ake fama da ita.

“Bari in fada muku, idan aka samu wannan karin, na rantse da Allah kwastomomi za su daina siyan simintin Idan suka daina kuma mu ne za mu yi asara ba su ba.

A nasa bangaren, wani dilan wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya koka kan yadda kamfanin na BUA zai kara farashin siminti ba tare da yin la’akari da talakawan Najeriya da ke sayen kayan domin yin gini ba.

A cewarsa, karin farashin ba zai tsaya a kan N200 a matakin dillalai ba, yace farashin zai iya haurawa zuwa N4, 000 a wajen ‘yan kasuwa na kasa-kasa

Ya bayyana cewa duk da cewa karin bai fara aiki a kan masu siye ba a yanzu ba, Amma idan kayan suka yi karanci a kasuwa, tabbas farashin zai tashi.

Dangane da ci gaban, wani babban dilan simintin na BUA a Kano, wanda ya bukaci a sakaya Sunan sa, ya nuna fushinsa kan lamarin.

A cewarsa, talakawa ne zasu Sha wahala da Wannan karin ,Amma ba mu Manyan diloli ba ,mu dai kawai mun san zamu samu ƙaranci Masu Siya.

Dilan ya yi mamakin yadda siminti na BUA ya karya alƙawarin da ta yi watannin baya cewa ba zai ƙara farashin simintin su ba, Amma gashi sun Kara har N200 gaskiya Wannan cin amanar Kasuwanci ne.

“Damuwata ita ce wannan Karin talakawa Masu Amfani da simintin abun Zai shafa Kuma in ya shafesu mu ma Zai shafe mu.

“Abin da ya daure min kai shi ne, a duk lokacin da wadannan kamfanoni suka yanke shawarar kara farashin kayan masarufi, za su yi shi ba tare da wani dalansu ya sani ba kuma da wuya su chanza matsayar da suka dauka ” ya koka.

Babban dillalin ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sa baki domin kawo karshen wahalar da ‘yan Najeriyar ke ciki

78 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...