Daily Nigerian, wata kafar yada labarai ta yanar gizo da ake bugawa a Najeriya, da mawallafin ta, Jaafar Jaafar, sun roki babbar kotun jihar Kano da ta umarci gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, da ya biya Naira miliyan 400 don biyan diyyar bata musu lokaci da kuma kokarin bata musu suna.
Ganduje, wanda ya gurfanar da duk wadanda ake zargin a kotu, yana neman diyyar bata masa suna, a ranar Talata ya nemi a dakatar da karar ba tare da bayar da wani kwakkwaran dalili ba.
Idan za’a iya tunawa Jaridar Daily Nigerian ta wallafa wani faifan bidiyo da ke nuna gwamnan yana karbar cin hanci daga hannun wani dan kwangila.

Amma lauyan jaridar Daily Nigerian, Muhammad Dan’Azumi, ya fadawa kotun cewa gwamnan ya bata lokacin Waɗanda yayi kara da kuma kokarin lalata mutuncin ta da cewa ta wallafa abubuwan batanci. Ya nemi diyyar naira miliyan 300.
Hakazalika, lauyan Jaafar, U. U. Eteng, ya nemi a ba shi naira miliyan 100.
Sun kuma bukaci kotun, ta umarci Ganduje da ya gabatar da sanarwar Hakurin kafin daukar duk wani mataki a kan lamarin.

Mai shari’a S. B. Namalam ya ba Ganduje takardar dakatar da shi, kuma ta umarce shi da ya biya kudin a kan N400,000 ga wadanda ake kara su biyu.