Yanzu-Yanzu: Majalisar Dokokin Kano ta dakatar da Muhuyi Magaji R/gado

Date:

Daga Sani Idris Mai waya

Majalisar Dokokin jihar Kano ta dakatar da Shugaban hukumar Karbar korafe-karafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin Gado, na tsawon wata guda.


 An dakatar da Muhuyi Magaji ne saboda kin amincewa da akawun da Akanta Janar na jihar kano ya tura Hukumar.


 Wannan ya biyo bayan wata takardar korafi ne a kansa da aka aike ta ofishin Babban Akanta Janar din.

 Wata wasika ta bayyana cewa Muhuyin ya nada Wani Ma’aikaci Mai matakin albashi na 4 a matsayin akawun hukumar, sabanin yadda Dokar Hukumar take.


 Shugaban masu rinjaye na Majalisar Alhaji Labaran Madari ya roki majalisar da ta mikawa kwamitin majalisar kan yaki da cin hanci da rashawa domin gudanar da bincike da kuma daukar mataki.


 Hakanan, Majalisar ta bukaci kwamitin da aka Mikawa batun da ya Mikawa Majalisar rahoton cikin makonni biyu.

93 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...