A hukumance kawo yanzu, shugaban hukumar zaɓen Najeriya INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya karɓi sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihohi huɗu.
Jihohi huɗun da aka gabatar da sakamakonsu a zauren taron sun haɗar da Ekiti da Kwara da Osun da kuma Ondo.
Sakamakon dai ya nuna dan takarar jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya samu nasara a jihohi uku watau Ekiti da Kwara da kuma Ondo.
A yayin da shi kuma dan takarar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya lashe zabe a jihar Osun.