Daga Rukayya Abdullahi Maida
Rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Kano ta gana da wakilan jam’iyyun APC NNPP da PDP domin a shawo kansu game da yakin neman zabe da jam’iyyun suka shirya gudanarwa yau Alhamis a Kano.
Kadaura24 ta rawaito Kwamishinan yan sanda na jihar kano CP Muhammad Yakubu ne ya jagoranci Zaman wanda aka yi shi da zummar sanar da su illar da yin tarukan nasu a rana guda zai haifar da Kuma yiyuwar samun matsala ga Zaman lafiya da ake da shi a Kano.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar yau Alhamis.
” Bayan samun labarin dukkanin wannan jam’iyyu guda uku suna son gudanar da tarukan yaƙin neman zabe a yau Alhamis, hakan tasa kwamishinan ‘yan sandan jihar kano CP Muhammad Yakubu ya gayyato wakilan jam’iyyun donin samun masalaha , Amma daga karshe dai masalahar bata Samu ba”. Inji
Kiyawa ya ce kwamishinan ya baiwa jam’iyyun shawarar dukkanin su su hakuri da yin taron, su bari sai bayan zaben Shugaban Kasa wanda za’a yi ranar Asabar Mai zuwa saboda kusancin da wuraren taron ke da shi ga na wata jam’iyyar.