Hukumar lura da aikin ‘yan sanda ta Najeriya ta maye gurbin Hajiya Naja’atu Mohammed, a matsayin ɗaya daga cikin masu sanya idanu na hukumar da za su lura da ayyukan ‘yan sanda a yankin arewa maso yammacin ƙasar a lokacin babban zaɓen ƙasar da ke tafe.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce an janyo hankalinta ne kan wata sanarwa da jam’iyyar APC mai mulki ta fitar, inda ta yi zargin cewa Hajiya Naja’atu na goyon bayan wata jam’iyya don haka APCn take gani ba za ta yi wa jam’iyyar adalci ba.
A sanarwar da APCn ta fitar mai ɗauke da sa-hannun daraktan yaɗa labaran yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Jam’iyyar Festus Keyamo ya yi watsi da naɗin Hajiya Naja’atu a matsayin mai lura da ayyukan ‘yan sanda a lokutan zaɓen ƙasar.
BBC Hausa ta rawaito Sanarwar da hukumar ‘yan sandan ta fitar ta ce ta maye gurbinta da tsohon mataimakin babban sifeton ‘yan sandan ƙasar Bawa Lawan domin lura da ayyukan ‘yan sanda a shiyyar ta arewa maso yamma.
Hukumar ta ce a kodayaushe tana taka-tsan-tsan a ayyukanta kuma za ta ci gaba da taimakawa wajen tabbatar da wanzuwar da dimokradiyya a ƙasar.
Haka kuma ta sake jaddada ƙudurinta na tabbatar da samun sahihin zaɓe a ƙasar.