Yanzu-Yanzu: An chanza kwamishinan ‘yan sandan jihar kano

Date:

Daga Auwalu Alhassan Kademi
Rundunar yan sanda ta kasa ta dauke kwamishinan ‘yan sandan jihar kano CP Mamman Dauda daga kano zuwa Jihar Filato.
Daily Nigeria ta rawaito Sanarwar da babban sufeton yan Sanda na kasa IGP Usman Alkali baba tace bayan mayar da CP Mamman Dauda zuwa jihar Filato an Kai CP Muhammad Yakubu zuwa Jihar Kano.
Talla
 A ranar Lahadin da ta gabata ne dai jam’iyyar NNPP ta yi barazanar fara zanga-zanga a fadin kananan hukumomin jihar Kano 44 domin nuna adawa da kamawa da tsare mambobinta har sama da 100, Inda ta zargi tsohon kwamishinan ‘yan sandan na Kano da nuna wariya ga yan jam’iyyar NNPP a Kano.
Talla daukar nauyi Hon. Surajo Umar Wudil
 Babban sufeton yan sanda na kasa din ya kuma tura manyan jami’an ‘yan sanda zuwa kowane gundumomi 109 na ‘yan majalisar dattawan kasar nan dake kasar nan a lokacin zabe.
 A wani sabon sako da aka fitar, IGP ya tura CP Ita Uku-Udom zuwa shiyyar Kano ta tsakiya; CP Sunday Babaji shiyyar Kano Arewa sai kuma DCP Abaniwonda Olufemi to Kano North.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...

Tinubu ka fadawa yan Nigeria Inda ka tsaya har kwana 5 bayan taron BRICS – ADC

    Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC ta soki Shugaban...

Da dumi-dumi: Yadda akai Jami’an tsaro suka kama ni -Danbello

Rahotannin sun tabbatar da cewa jami'an tsaro a Nigeria...