Chanjin kudi: Akwai bukatar mawadata su tallafawa mabukata – Munzali Sani Musa

Date:

Daga Kamal Yakubu Ali

 

Wani dan kasuwa a nan kano Alh munzali Sani Musa ya bukaci mawadata dake cikin al’umma dasu tallafawa mabukata gwargwadon iko duba da halin matsi da al’umma  ke ciki musamman da abinda zasu cigaba da gudanarda da rayuwarsu.

 

Kadaura24 ta rawaito Alhaji munzali sani Musa ya bayyana hakanne a yayin da yake ganawa  da manema labarai a ofishinsa.

 

Ya ce yawan sadaka da kyauta baya rage yawan dukiya, sai dai ya kara habbaka ta  kamar yadda Allah subhanahu wata Allah ya bayyana a cikin Alkurani mai girma, cewa duk abinda ka bayar zai dawo maka dashi.

Talla

“Ku  taimakawa al’umma da abun da Allah ya hore muku domin rage musu radadin halin da suke ciki , idan kukayi hakan Allah zaiyi farin ciki da hakan” . Inji Alh. Munzali Sani

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

Ya kuma Kara da cewar Annabi sallallah Alaihi wasallam yace kayi sadaka koda da barin dabino ne, ka baiwa dan uwanka shi ma. Allah yana farin ciki da hakan.

 

Yace mutukar mawadata dake jihar nan suka jajirce wajan tallafawa yan uwansu da sauran al’umma dake tare dasu, babu shakka za a sami sauki a halin Kunchi da ake ciki musamman ta hanyar samar musu abincin da sauran bukatun sa na yau da kullum.

Ya bayyana cewa duk wanda Allah ya yalwata masa da dukiya babban abinda zai yi wajan ganin dukiyar nan ta dawwama shi ne tallafawa mubakata ta fannoni da dama, Hakika Allah zai sanya Albarka a wannan dukiya dama zuriarsa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...