Atiku ya mayar da martani ga Tinubu kan zargin ƴan adawa ne su ka haifar yunwa a Nijeriya

Date:

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya zargi Shugaba Bola Tinubu da ƙoƙarin kauce wa alhakin matsin tattalin arzikin da ’yan Najeriya ke fuskanta, bayan shugaban ya zargi ’yan adawa da haddasa yunwa da talauci a ƙasar.

A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku na ADC, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya kwatanta maganar Tinubu da mutumin da ya kunna wuta sannan ya zargi maƙwabtansa da hayaƙin da ta haifar.

IMG 20260704 WA0007
Talla

Atiku ya ce jam’iyyar APC ta shafe shekaru takwas tana mulkin Najeriya kafin Tinubu ya hau karagar mulki, kuma gwamnatin yanzu ta ƙara kusan shekaru uku da rabi, don haka bai kamata ta ɗora wa ’yan adawa alhakin matsin rayuwa ba.

Ya tambayi gwamnatin Tinubu kan cire tallafin man fetur, faduwar darajar naira, ƙaruwar talauci da matsalar tsaro da suka haɗa da kashe-kashe, garkuwa da mutane da korar al’umma daga muhallansu.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi tambayoyi kan wasu kuɗaɗen gwamnati da ya ce suna buƙatar bayani, ciki har da kashe-kashen da suka shafi tsaron makamashi da ayyukan bututun mai na NNPC.

Atiku ya ce ya kamata a auna nasarar gwamnati bisa yanayin rayuwar ’yan Najeriya, ba wai bayanan da take bayarwa a wajen tarukan siyasa ba.

FB IMG

Ya bayyana zaɓen shugaban ƙasa na 2027 a matsayin damar da ’yan Najeriya za su yi amfani da ita wajen yanke hukunci kan ayyukan gwamnatin Tinubu.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

‎2027: Ɗan Takarar ADC na Wudil da Garko ya Bayyana Manufofinsa a Taron Muhawarar da aka shirya musu

‎Ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai na ƙananan hukumomin Wudil...

‎2027: APC ta baiwa Gwamna Abba Tutar Takarar Gwamnan Kano

‎Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya halarci...

2027: Tinubu ya zargi ’yan adawa da haddasa yunwa da talauci a Najeriya

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya zargi ’yan adawarsa da...

Yawan Mutanen da su ka je taron APC na Kaduna ya nuna Tinubu zai ci zabe a 2027 – Kwankwaso

 Wani jigo a jam’iyyar APC, Musa Illiyasu Kwankwaso, ya...