‎2027: Ɗan Takarar ADC na Wudil da Garko ya Bayyana Manufofinsa a Taron Muhawarar da aka shirya musu

Date:

‎Ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai na ƙananan hukumomin Wudil da Garko a ƙarƙashin tutar jam’iyyar ADC, Hon. Barrister Ahmad Sani Bawa, ya bayyana manufofinsa da shirye-shiryensa na inganta rayuwar al’ummar yankin idan aka zaɓe shi.
‎
‎Barrister Ahmad Sani Bawa ya bayyana hakan ne yayin wani taron muhawara da Ƙungiyar Ci gaban Matasa ta Ƙaramar Hukumar Garko ta shirya, domin bai wa ’yan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya damar gabatar da manufofinsu a gaban al’umma.

IMG 20260704 WA0007
Talla

‎
‎A yayin taron, ɗan takarar ya bayyana cewa babban burinsa shi ne samar da ingantaccen wakilci da zai mayar da hankali kan ci gaban matasa, inganta harkokin ilimi da lafiya, tare da tallafa wa manoma da mata domin bunƙasa tattalin arzikinsu.
‎
‎Ya jaddada cewa idan al’ummar Wudil da Garko suka ba shi damar wakiltarsu, zai yi ƙoƙarin tabbatar da cewa wakilcinsa ya amfani kowa, ba tare da nuna bambancin jam’iyya ko yanki ba.
‎
‎Haka kuma, Barrister Bawa ya tabbatar da aniyarsa ta mutunta yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma tsakanin ’yan takarar, yana mai cewa zai gudanar da yaƙin neman zaɓensa cikin lumana, tare da guje wa cin mutunci ko ɓata sunan sauran ’yan takara.
‎
‎Taron dai ya gudana cikin kwanciyar hankali, inda aka bai wa kowane ɗan takara damar bayyana manufofinsa da shirye-shiryensa ga al’ummar yankin.

‎
‎A nasu ɓangaren, wasu daga cikin masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun yaba da yadda Barrister Bawa ya gabatar da magufofinsa yayin muhawarar, suna mai bayyana cewa natsuwa da yadda ya gabatar da manufofinsa na daga cikin abubuwan da suka lura da su a yayin taron.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Atiku ya mayar da martani ga Tinubu kan zargin ƴan adawa ne su ka haifar yunwa a Nijeriya

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya zargi...

‎2027: APC ta baiwa Gwamna Abba Tutar Takarar Gwamnan Kano

‎Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya halarci...

2027: Tinubu ya zargi ’yan adawa da haddasa yunwa da talauci a Najeriya

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya zargi ’yan adawarsa da...

Yawan Mutanen da su ka je taron APC na Kaduna ya nuna Tinubu zai ci zabe a 2027 – Kwankwaso

 Wani jigo a jam’iyyar APC, Musa Illiyasu Kwankwaso, ya...