Jam’iyyar PDP ta ce ta karɓi hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta soke zaɓen fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar domin zaɓen ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe na 2027.
Kotun ta kuma umarci jam’iyyar da ta gudanar da sabon zaɓen fidda gwani cikin wa’adin wata guda.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na PDP a Jihar Gombe, Abdulkadir Ahmed Dukku, ya fitar, jam’iyyar ta ce tana mutunta hukuncin kotun tare da sake jaddada aniyarta ta bin doka da oda da kuma mutunta ‘yancin bangaren shari’a.
Jam’iyyar ta bayyana cewa shugabancinta na nazarin hukuncin a hankali domin fahimtar abubuwan da ya ƙunsa da kuma umarnin da kotun ta bayar.
Saboda haka, PDP ta yi kira ga mambobinta, magoya baya da sauran masu ruwa da tsaki a Jihar Gombe da su kasance cikin nutsuwa, haƙuri da haɗin kai, tare da guje wa yada jita-jita ko kalaman da za su iya haddasa tashin hankali.
Ta kuma buƙaci mambobinta da su jira ƙarin umarni daga shugabannin jam’iyyar bayan kammala nazarin hukuncin tare da samun shawarwarin lauyoyin jam’iyyar.
PDP ta ce za ta ɗauki dukkan matakan da doka ta tanada domin kare muradunta na halal da kuma tabbatar da mutuncin tsarin dimokuraɗiyyar jam’iyyar.
Read also: Yadda Wani Mai Sana’ar POS a Kano ya Mayar da Miliyan 10 da aka Tura Masa Bisa Kuskure
Read also: Yadda USAID ke ɗaukar nauyin Boko Haram —Dan Majalisar Amurka

Jam’iyyar ta ƙara kira ga masu ruwa da tsaki da su ci gaba da nuna haƙuri da zaman lafiya yayin da ake ci gaba da tafiyar da lamarin bisa tanadin doka da kundin tsarin jam’iyyar.
“Muna nan daram kan dimokuraɗiyya da Jam’iyyar Peoples’ Democratic Party,” in ji sanarwar.