‎Gidauniyar Festula ta tallafa wa mata 50 da suka warke daga lalurar yoyon fitsari

Date:


‎Gwamnatin Jihar Kano ta ce tana ci gaba da wayar da kan al’umma kan buƙatar daina kyamar matan da suka kamu da lalurar yoyon fitsari.

‎Gwamnatin ta ce kyamar da wasu mata masu fama da wannan lalura ke fuskanta na ƙara jefa su cikin damuwa tare da ware su daga cikin al’umma.

‎Wakiliyar Kwamishiniyar Harkokin Mata ta Jihar Kano, Dr Halima B. B. Faruk, ce ta bayyana hakan yayin bikin rabawa mata 50 da suka warke daga yoyon fitsari kayan sana’o’i da Gidauniyar Festula Foundation ta shirya.

FB IMG

‎Dr Halima ta ce gwamnatin jihar na farin ciki matuka da yadda matan suka samu kulawa da magani har suka warke daga lalurar.

‎Ta ce baya ga yi musu magani, an kuma koyar da matan sana’o’i tare da ba su kayan aikin sana’ar, domin su samu damar dogaro da kansu.

‎Ta buƙaci matan da su yi amfani da kayan sana’ar da aka ba su yadda ya kamata, domin su inganta rayuwarsu da ta iyalansu.

‎Dr Halima ta ƙara da cewa gwamnatin Jihar Kano za ta ci gaba da tallafa wa mata masu fama da lalurar yoyon fitsari a faɗin jihar, tare da samar da duk wani taimakon da ake buƙata domin su samu kulawar da ta dace.

‎A nasa jawabin, Shugaban Festula Foundation, Baba Musa Isah, ya ce gidauniyar na tallafa wa mata masu fama da lalurar yoyon fitsari a sassa daban-daban na Najeriya.

‎Ya ce gidauniyar na yi wa matan tiyata kyauta ba tare da karɓar kuɗin aikin ba.

‎Baba Musa ya ce bayan an yi wa matan magani, gidauniyar na koyar da su sana’o’i tare da ba su kayan aiki, domin su samu damar dogaro da kansu.

‎Ya ce matan da aka tallafa wa a wannan karon duk ’yan Jihar Kano ne, kuma yanzu za su koma cikin al’umma domin ci gaba da rayuwarsu.

‎Shugaban gidauniyar ya ce duk da ƙoƙarin da ake yi wajen magance matsalar, har yanzu ana samun sabbin masu fama da lalurar yoyon fitsari.

IMG 20260728 WA0005
Talla


‎Ya ce hakan ne ya sa gidauniyar ke ci gaba da ziyartar jihohin Najeriya domin yi wa masu fama da lalurar magani tare da wayar da kan al’umma kan hanyoyin kariya da muhimmancin neman magani.

‎Ya ƙara da cewa, kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana, ana…

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Kwankwaso ya buɗe ƙofar sulhu da Abba Gida-Gida

‎ ‎Jagoran Ƙungiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana...

‎Gwamna Abba ya taya Radio Kano murnar cika shekaru 80

‎ ‎Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya taya...

‎Kungiyar Nigeria Forward ta bukaci Arewa ta mutunta tsarin karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu

‎ ‎Ƙungiyar Nigeria Forward (NF) ta yi kira ga al’ummar...

‎Kungiyar Nigeria Forward ta bukaci Arewa ta mutunta tsarin karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu

‎Ƙungiyar Nigeria Forward (NF) ta yi kira ga al’ummar...