Gwamnatin Kano ta ba da hutun Maulidi

Date:

Gwamnatin Kano ta ayyana Talata, 1 ga Satumba, 2026, a matsayin ranar hutu domin bai wa al’ummar jihar damar gudanar da bikin Takutaha.

Sanarwar hakan tana kunshe ne cikin sanarwar da babban sakatare na Ma’aikatar Kafa Hukumomi, Abba A. Danguguwa, ya sanya wa hannu a madadin Shugaban Ma’aikatan Jihar.

IMG 20260704 WA0007
Talla

A cewar sanarwar, ranar hutun ta yi daidai da 19 ga Rabi’ul Awwal, 1448AH, kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya amince da ita.

Gwamnatin ta bayyana Takutaha a matsayin muhimmiyar al’ada da ke da matukar muhimmanci ga al’ummar Kano, tare da cewa bikin wani bangare ne na tarihin Musulunci a jihar.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gidauniyar Barau Ta Karyata Zargin Biyan Tallafin N50,000 Duk Wata Ga Daliban FUDMA

Gidauniyar Barau I. Jibrin ta karyata wani rahoto da...

‎Gwamnatin Kano Za Ta Mayar da Gidan Rediyon Jihar Cibiyar Horar da Ma’aikatan Kafafen Yaɗa Labarai

‎ ‎Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana aniyarta ta sauya tsarin...

Kungiyar Matasan Gidan Nasiru Gawuna Sun Koma Goyon Bayan Abba Gida-Gida

Kungiyar matasa masu goyon bayan tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar...