Gidauniyar Barau Ta Karyata Zargin Biyan Tallafin N50,000 Duk Wata Ga Daliban FUDMA

Date:

Gidauniyar Barau I. Jibrin ta karyata wani rahoto da ke zargin cewa tana bin wasu ɗaliban da suka ci gajiyar shirin tallafin karatu na jami’ar Federal University Dutsin-Ma (FUDMA) kuɗaɗen alawus.

A wata sanarwa da Ismail Mudashir, Mai Ba Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Shawara kan Yaɗa Labarai, ya fitar a ranar 26 ga Agusta 2026, ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya da yaudara, yana mai cewa an ƙirƙire shi ne domin ɓata sunan shirin tallafin karatun.

IMG 20260704 WA0007
Talla

Sanarwar ta ce Gidauniyar Barau I. Jibrin ta bai wa ɗalibai marasa ƙarfi 810 tallafin karatu domin su gudanar da karatun digiri ta cibiyoyin karatu guda shida na FUDMA da ke yankin Kano ta Arewa.

A watan Yunin 2026, lokacin da jami’ar ta gayyaci ɗaliban zuwa babban harabarta da ke Dutsin-Ma, Jihar Katsina, domin gudanar da horo kan tsarin karatun nesa, an bai wa kowane ɗalibi N50,000 a matsayin tallafin sau ɗaya.

Haka kuma, gidauniyar ta dauki nauyin jigilar ɗaliban zuwa Dutsin-Ma, inda horon ya ɗauki tsawon makonni huɗu.

Gidauniyar ta jaddada cewa ba ta taɓa yin alkawarin biyan N50,000 a kowane wata ga ɗaliban ba. Ta ce kuɗin N50,000 da aka bayar an ware su ne musamman domin tallafa wa ɗaliban yayin horon na makonni huɗu.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa shirin tallafin karatun ya ƙunshi biyan kuɗaɗen rajistar ɗaliban daga matakin farko har zuwa kammala karatunsu na digiri.

IMG 20260704 WA0005
Talla

Gidauniyar ta buƙaci ɗaliban da suka amfana da shirin da su mayar da hankali kan karatunsu tare da yin watsi da rahoton da ta bayyana a matsayin yunƙurin raba hankalinsu da kuma zubar da mutuncin shirin.

Gidauniyar Barau I. Jibrin ta sake tabbatar da aniyarta ta ci gaba da tallafa wa ɗalibai marasa ƙarfi da kuma faɗaɗa damar samun ingantaccen ilimi a Kano ta Arewa da sauran sassan ƙasar.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

‎Gwamnatin Kano Za Ta Mayar da Gidan Rediyon Jihar Cibiyar Horar da Ma’aikatan Kafafen Yaɗa Labarai

‎ ‎Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana aniyarta ta sauya tsarin...

Gwamnatin Kano ta ba da hutun Maulidi

Gwamnatin Kano ta ayyana Talata, 1 ga Satumba, 2026,...

Kungiyar Matasan Gidan Nasiru Gawuna Sun Koma Goyon Bayan Abba Gida-Gida

Kungiyar matasa masu goyon bayan tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar...