Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce zaɓen 2027 ba zai kasance zaɓe tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da “takarce” ba, sai dai zaɓe ne tsakanin ƙwato mutanen Kano daga hannun waɗanda ya kira “’yan fasa-fasa, mu sha ruwan kwai”.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karɓar baƙuncin shugabannin ƙungiyar APC Intellectual Door-to-Door Awareness Forum, wadda ta kai masa ziyara.

Waiya ya ce al’ummar Kano a yanzu ba makafi ba ne, domin idonsu ya buɗe kuma sun fahimci irin shugabancin da suke so. Ya ƙara da cewa duk wani yunƙuri na kawo wasu mutane a matsayin waɗanda za su tsaya takarar gwamna a 2027 ba zai ruɗi al’ummar jihar ba.
A cewarsa, “Al’ummar Kano sun san Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin ɗan takarar gwamna, ba ‘yan fasa-fasa, mu sha ruwan kwai ba.”
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa ma’aikatarsa za ta samar da wani tsari na musamman da zai bai wa ƙungiyoyi irin wannan damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, tare da ci gaba da wayar da kan jama’a kan nasarorin da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta samu.
Ya ce wannan zai taimaka wajen ganin an samu nasarar jam’iyyar a zaɓen 2027 da ke tafe
A nata jawabin, shugabar ƙungiyar, Hajiya Hauwa, ta ce sun shirya tsaf domin ganin jam’iyyar APC ta samu nasara daga sama har ƙasa a zaɓukan da ke tafe.
Hajiya Hauwa ta yabawa Kwamishinan bisa yadda yake karɓar ƙungiyoyi daban-daban da kuma yadda yake sauraron bukatunsu tare da basu kulawar da ta dace.
Ta ce irin wannan hulɗa tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin al’umma na taimakawa wajen ƙarfafa haɗin kai da fahimtar juna.