Rundunar Tsaron Fararen Hula ta Ƙasa (NSCDC) ta tura jami’ai 10,210 domin karfafa tsaro yayin zaben gwamnan jihar Osun da za a gudanar ranar Asabar.
Mai magana da yawun rundunar, Babawale Afolabi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja.
Ya ce daga cikin jami’an da aka tura, 10,000 jami’an aiki ne, yayin da sauran 210 suka fito daga sassan leken asiri da rundunonin dabarun musamman.

Afolabi ya ce an kuma janye jami’ai 1,000 daga rundunonin NSCDC na jihohi 10 domin su taimaka wajen tabbatar da tsaro a lokacin zaben.
Ya bayyana cewa an tura rundunonin musamman da suka hada da tawagar leken asiri ta musamman, SWAT, tawagar mata ta musamman, Mining Marshals, Special Strike Force, Crack Squad da rundunar karnukan bincike ta K9.
A cewar NSCDC, rundunonin za su mayar da hankali kan tattara bayanan sirri, dakile laifuka, kare muhimman kadarori, kula da cunkoson jama’a da kuma sauran ayyukan tsaro da suka shafi zaben.
Rundunar ta gargadi ‘yan daba da masu shirin tayar da tarzoma ko kawo cikas ga gudanar da zaben cikin lumana da cewa za su fuskanci hukunci kamar yadda dokar zabe ta tanada.
Kwamandan NSCDC na jihar Osun, Igbalawole Sotiyo, ya bukaci jami’an rundunar da su kasance masu tsaka-tsaki, kada su shiga harkokin siyasa, tare da gudanar da ayyukansu cikin kwarewa da mutunta hakkin jama’a.

Ya ce jami’an tsaro na da alhakin samar da yanayi mai kyau da tsaro domin ‘yan kasa su gudanar da hakkinsu na kada kuri’a cikin kwanciyar hankali ba tare da tsoro ko tsangwama ba.
Sotiyo ya kuma bukaci jama’a da su hada kai da jami’an tsaro tare da kai rahoton duk wani abu da ake zargi da ka iya kawo barazana ga zaman lafiyar zaben.