‎Ana zargin Gwamnatin Kano ta ware makuden kudade domin gina makarantu, Amma an neme su an rasa

Date:


‎Ƙungiyar da ke bibiyar aiwatar da kasafin kuɗi a Najeriya ta Tracka ta rahotanni da hada sun nuna an ware ko an biya kuɗaɗe ga wasu ayyuka a jihar Kano da ake cewa ba a same su a wurin da aka ce an aiwatar da su ba.

‎ Kungiyar ta wallafa bayanan da ke zargin cewa gwamnatin ta Kano ta ware miliyoyin kudaɗe a kasafin kudin 2025 amma ba a ga ayyukan ba.

‎A ranar 5 ga Agusta 2026, ƙungiyar da ke bibiyar aiwatar da kasafin kuɗin a Najeriya ta yi zargin cewa an fitar da fiye da naira biliyan ɗaya domin gyaran azuzuwa 100 a faɗin jihar ta Kano amma kuma ba a gano wurin da makarantun suke ba.

IMG 20260704 WA0007
Talla


‎Har wa yau, Tracka ta kuma yi batun ƙarin wasu naira miliyan 235 da aka ware domin gina wata makaranta a ƙaramar hukumar Sumaila amma kuma babu ita babu labarinta.

‎Ƙungiyar da ke bibiyar aiwatar da kasafin kuɗin, a shafinta na Facebook ta ce kasafin kuɗin jihar Kano na 2025 ya ware fiye da naira miliyan 235 domin gina azuzuwa a wata makaranta a ƙaramar hukumar Sumaila.

‎A cewar rahoton Aiwatar da kasafin Kuɗi na zango na huɗu na jihar Kano na shekarar 2025, an biya Naira miliyan 235.4 domin gina azuzuwa biyu masu hawa ɗaya, kowannensu ɗauke da ajujuwa huɗu tare da ofis da ɗakin ajiya, a makarantar mata ta sakandare ta gwamnati, da ke Massu a ƙaramar hukumar Sumaila ta Jihar Kano,” in ji bayanin na Tracka.

‎Tracka ta kuma ƙara da cewa jami’anta sun ziyarci Massu domin ganewa idanunsu yadda aikin ya gudana.

‎”Mun ziyarci al’ummar Massu a watan Yunin 2026, amma ba wai kawai ba mu ga wannan aikin ba, har ma mazauna yankin sun ce babu wata makaranta mai suna GGSSS a garin Massu. Haka kuma mun kai ziyara wasu ƙauyuka da ke gundumar Massu, amma ba mu samu wata makaranta mai wannan suna a duk faɗin yankin Massu ba.”

Gidan Radio Express ya magantu kan bidiyon rikicin Nagoda da Baban Lungu

‎Bugu da ƙari, Tracka ta ƙara da nuna damuwa dangane da yadda ta nemi wasu ayyukan gyaran azuzuwa 100 a faɗin jihar da aka ware musu tsabar kuɗi har naira biliyan ɗaya, da aka ce ba a san takamaiman wurin da za a yi aikin ba.

‎” A cewar Rahoton aiwatar da Kasafin Kuɗi na zango na huɗu na jihar Kano na shekarar 2025, an fitar da sama da Naira biliyan 1 domin gyaran ajujuwa 100 a faɗin jihar,” in ji Tracka.

‎Sai dai kuma Tracka ta ce ta nemi bayani dangane da makarantun da wuraren da ake aikin nasa amma ba su samu gamsasshen bayani ba.

‎”Mun aike da buƙatar samun bayanai ƙarƙashin Dokar ‘Yancin Samun Bayanai (FOI) ga Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar Kano (SUBEB) a watan Mayun 2026. Amma a martaninta, hukumar ta ce ba ta da bayanan wuraren da aka gudanar da gyaran ajujuwan.”

‎”Makaranta ɗaya tilo da hukumar ta nuna mana ita ce Makarantar Firamare ta Jili da ke Rimin Gado, inda muka tabbatar cewa an yi mata fenti tare da wasu gyare-gyare. Daga nan ne aka shawarce mu mu tuntubi Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano domin samun bayanai kan wuraren da aka aiwatar da wannan aikin,” in Tracka.

‎BBC ta tuntuɓi gwamnatin Kanon domin jin bahasinta dangane da wannan batu, inda kuma ta ce ba haka batun yake ba, tana mai bayyana shi da jita-jita.

‎Daraktan yaɗa labaran gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya shaida wa BBC cewa bisa bayanan da ya samu daga ƙaramar hukumar Sumaila da ma’aikatar ƙananan hukumomin jihar babu wannan al’amari a cikin kasafin kuɗinsu.

‎”Hasalima ba ya cikin abubuwan da ƙaramar hukumar ta taɓa rubutowa a ba ta, kuma ba ya cikin abin da ƙaramar hukumar ta karɓa a hannun gwamnatin jiha domin ta yi,” in ji shi.

‎Mai magana da yawun gwamnan jihar ya kara da cewa hasalima Shi gini ko gyaran makarantar sakandire alhakin gwamnatin jiha ne, ba na ƙaramar hukuma ba.

‎”Mafi akasari ƙananan hukumomi suna samu amincewa gwamnatin jiha ne, domin su yi gyara ko gina sababbin makarantun furamare, amma ba sakandire ba, sai dai in akwai wata bukatar gyaran sakandire da wataƙila karamar hukumar ke ganin za ta iya gyara wa bisa raɗin kanta da kuɗaɗenta”, in ji shi.

‎Kakakin gwamnan ya ci gaba da cewa ma’aikatar ilimin jihar Kano ba ta taɓa gabatar da wani aiki da ya shafi wannna makaranta ba.

IMG 20260728 WA0005
Talla


‎Sai dai ya ce wataƙila aikin mazaɓa ne da wani ɗanmajalsia ya gabatar a matsayin abin da za a sanya cikin kasafin kuɗi, amma ba ya cikin ayyukan da ma’aikatar ilimin jihar da gabatar ba.

‎Ya yi zargin cewa irin ƙungiyoyin da ke gabatar da wanan bincike suna yi aiki ne da jita-jita.

BBC Hausa

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba ya jagoranci daurin auren gata na zawarawa da ’yan mata 1,500 a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci...

Gidan Radio Express ya magantu kan bidiyon rikicin Nagoda da Baban Lungu

 Hukumar Express Radio Nigeria tana sanar da al’umma cewa...

NEPC ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki tare da rabon ingantattun tsiron Cashew a Kano.

Hukumar Bunƙasawa tare da Fitar da Kayayyakin ta Najeriya,...