Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Dr. Umar Farouk ya bukaci Sarkin Takutahar Kasar Hausa Sheikh Abdulkadir Jiyali yayi dukkan abunda ya kamata domin kawowa Najeriya cigaba.
Sarkin na Daura ya bukaci hakan ne lokacin da ya ke nada shi a Matsayin Sarkin Takutahar Kasar Hausa na farko a tarihin Masautun Kasar Hausa a Najeriya.

Alhaji Dr. Umar Farouk yace Sheikh Jiyali ya cancanci bashi wannan sarauta ne bisa la’akari da yadda yake hidimtawa Al’uma da cusawa Matasa Soyayyar Annabi Muhammadu SAW.
Adon haka ne Sarkin na Daura ya bukaci Sarkin Takutahar ya cigaba da Mai da hankali ga dukkan abunda zai kawo Zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin Al’uma.
Alhaji Dr. Umar Farouk yayi kira da ya cigaba da yin biyayya bisa ga wannan Shugabanci da aka dora masa tareda hada kan Matasa.

A nasa bangren Sarkin Takutahar Kasar Hausa Sheikh Jiyali Abdulkadir ya godewa Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Dr. Umar Farouk bisa wannan Sarauta da aka nadashi tareda tabbatar da cewa zai dora tareda jajircewa akan yadda aka Saba Da Qara Tsabtace Ita Kanta Harkar Takurahar.