Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Kananan hukumomin Sumaila/Takai, Barrista Rabiu Ibn Yusuf, ya yabawa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa irin salon jagoranci da ayyukan ci gaban da gwamnatinsa ke aiwatarwa, inda ya bayyana shi a matsayin gwamna mai son aiki kuma mai jajircewa wajen inganta rayuwar al’umma.
A cikin wata sanarwa, Barrista Rabiu Yusuf ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jajirce wajen sauya fasalin jihar ta hanyar aiwatar da ayyukan raya ƙasa da suka shafi fannoni daban-daban da suka haɗa da ilimi, lafiya, ababen more rayuwa, noma, ƙarfafa matasa da mata, da walwalar al’umma.

Ya ce cikin shekaru uku da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta shafe tana mulki, an aiwatar da muhimman ayyuka da suka haɗa da gyaran makarantu da gina sababbi, inganta cibiyoyin lafiya, samar da kayan koyo ga ɗalibai, da kuma shirye-shiryen bunƙasa ilimi da kiwon lafiya.
Hakazalika, ya yaba da yadda gwamnatin ta mayar da hankali wajen gina da gyaran tituna, magudanan ruwa da sauran ababen more rayuwa a sassa daban-daban na jihar, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen sauƙaƙa zirga-zirga da bunƙasa harkokin tattalin arziki.
Da dumi-dumi: Kotu ta soke rajistar jam’iyyar NDC ta su Kwankwaso
Barrista Rabiu Yusuf ya kuma yabawa gwamnan kan shirye-shiryen tallafa wa matasa da mata ta hanyar horas da su sana’o’i, bayar da tallafin dogaro da kai, guraben karatu da kuma tallafa wa ƙananan da matsakaitan ‘yan kasuwa.
A cewarsa, gwamnatin ta kuma ba da muhimmanci ga bunƙasa rayuwar ɗan Adam ta hanyar ɗaukar nauyin karatun ɗalibai a gida da ƙasashen waje, tare da aiwatar da shirye-shiryen rage rashin aikin yi da talauci.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da fifita jin daɗin al’umma ta hanyar manufofin da ke ƙarfafa haɗin kai, bunƙasa tattalin arziki da ci gaba mai ɗorewa.

Daga ƙarshe, Barrista Rabiu Yusuf ya yi kira ga al’ummar Jihar Kano da su ci gaba da bai wa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf goyon baya domin ci gaba da aiwatar da ayyukan raya jihar.
> “Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna nagartaccen jagoranci da jajircewa wajen ci gaban Jihar Kano. Bisa irin ayyukan ci gaban da gwamnatinsa ta aiwatar, ya cancanci yabo a matsayin gwamna mai son aiki kuma mai sadaukar da kansa wajen yi wa al’umma hidima,” in ji Barrista Rabiu Ibn Yusuf.