Babbar kotun tarayya da ke Lokoja a jihar Kogi ta soke hukuncin da ta yanke a baya wanda ya umarci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta yi wa jam’iyyar NDC rajista a matsayin jam’iyyar siyasa kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Mai shari’a Isah Dashen ya yanke hukuncin ne a ranar Juma’a, inda ya ce dole ne a saurari dukkan bangarorin da abin ya shafa kafin a yanke hukunci a kan lamarin.

Kotun ta amince da bukatar jam’iyyar PMP, wadda ta ce tana da ruwa da tsaki a shari’ar. Alkalin ya bayyana cewa hukuncin da aka yanke a watan Disamban 2025 ya samu nakasu saboda ba a saurari dukkan masu ruwa da tsaki ba.
Kotun ta umarci a mayar da al’amura yadda suke kafin hukuncin da aka yanke a ranar 10 ga Disamba, 2025, tare da ba da umarnin a sake fara sauraron shari’ar daga farko.
AHIP ta gargaɗi matasa kan illar miyagun ƙwayoyi, ta nemi iyaye su ƙara kula da ‘ya’yansu
Lauyan PMP, Chikezie Ekeocha, ya ce jam’iyyar ta garzaya kotu ne bayan gano cewa NDC ta yi amfani da tambarin da PMP ta gabatar wa INEC tun kafin a fara shari’ar.

Ya bayyana cewa hukuncin kotun na nufin dakatar da duk wani mataki da INEC ta dauka dangane da rajistar NDC, ciki har da takardar rajista da sanya jam’iyyar cikin bayanan hukumar, har sai an kammala shari’ar.
Sai dai lauyan ya jaddada cewa har yanzu ba a yanke hukunci na karshe a kan shari’ar ba, domin kotun ta bukaci a hada dukkan bangarorin da abin ya shafa kafin ta sake yanke sabon hukunci.