A yau ne aka ci gaba da rabon Takin Noma na Zamani kyauta ga manoma a ƙananan hukumomin Kabo, Bagwai da Dawakin Tofa, a matsayin wani ɓangare na shirin tallafa wa harkokin noma da inganta samar da abinci.
Shirin, wanda Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, CFR, ya ɗauki nauyi, na ci gaba da kawo sauƙi ga dubban manoma a yankin Kano ta Arewa ta hanyar samar musu da takin noma ba tare da sun biya komai ba.

Manoman da suka amfana sun bayyana farin cikinsu kan wannan tallafi, suna mai cewa zai taimaka musu wajen ƙara yawan amfanin gona tare da rage musu nauyin kashe kuɗaɗen noma.
Wannan shiri na daga cikin ƙoƙarin Sanata Barau na ƙarfafa fannin noma, inganta rayuwar al’umma, da kuma tallafawa manufofin samar da wadataccen abinci a ƙasa.