Zaben Cike Gurbi: Rundunar yansandan Kano ta bayyana shirinta

Date:

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano ta bayyana matakan tsaro da aka amince da su gabanin zaben cike gurbin ɗan majalisar Tarayya mai wakiltar Dawakin Kudu da Warawa wanda zai gudana ranar Asabar.

Wannan na ƙunshe cikin wata sanarwa da kakakin rundunar,CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar.

IMG 20260504 WA0036(1)
Talla

Yace bisa umarnin kwamishina CP Ibrahim Adamu Bakori an takaita zirga-zirga a yankunan da za a gudanar da zaben daga karfe 12am zuwa ƙarfe 5pm a ranar Asabar, in banda jami’an da aka amince dasu.

Yace an tura isassun jami’an tsaro yankin domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi tare da sanya idanu kan yadda zaben zai gudana.

Sanarwar ta bukaci masu zabe su fito cikin lumana domin gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

IMG 20251224 WA0004

Rundunar ta ayyana cewa ba za ta lamunci tashin hankalin zaɓe, siya ko sayar da ƙuri’a, kwace akwatunan zaɓe, tsoratar da masu zaɓe, da kuma yaɗa labarai na ƙarya ba.

Duk wanda aka samu yana aikata wani nau’in magudin zaɓe za a kama shi kuma a gurfanar da shi a gaban kuliya bisa ga Dokar Zaɓe ta 2022.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sabuwar Takaddama: Gwarzo Ya Kalubalanci Gwamnatin Kano Kan Zargin Cin Hanci

‎ ‎ ‎Dan takarar gwamna na jam’iyyar NDC a Jihar Kano...

Shugaba Tinubu ya daga likafar hadiminsa Abdulaziz Abdulaziz

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙara wa Malam...

‎Majalisar Wakilan Najeriya ta bukaci Tinubu ya inganta tsaro ko ya yi murabus

‎‎ ‎Ɓangaren marasa rinjaye a Majalisar Wakilan Najeriya ta yi...

Sanata Barau Ya Rabawa ’Yan Sandan Kano Ta Arewa Mashina 1,000 Domin Inganta Tsaro

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya sake nuna...